DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya na da isassun kuɗin da Shugaba Tinubu zai yi tafiye-tafiye kasashen duniya – Ministan harkokin waje

-

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar, ya ce Nijeriya na da isassun kuɗin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa kasashen ketare.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa da gidan talabijin na Channels ke gabatarwa.

Google search engine

Wasu ‘yan Nijeriya dai na yin guna-guni kan yadda shugaban kasar ke yin balaguro daga kasa zuwa kasa, ba tare da kasar ta samu wani ci gaba ba.

Sai dai Ministan ya yi watsi da wannan, inda yace ziyarar shugaban ta jawo wa Nijeriya masu zuba hannun jari da suka saka dala biliyan 2 bayan ziyarar da ya kai a ƙasar Brazil.

Tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2023, rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya ziyarci kasashe kusan 19 a tafiye-tafiye 32 kasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kotu ta ba jam’iyyar PDP izinin gudanar da taronta na kasa a Ibadan

Babbar kotun jihar Oyo da ke Ibadan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. L. Akintola, ta bai wa jam’iyyar PDP damar gudanar da babban taronta na...

Gwamnan Katsina Radda ya gabatar da kasafin 2026 na Naira biliyan 897

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2026 wanda ya kai Naira biliyan 897.8 a zauren majalisar...

Mafi Shahara