Monday, April 6, 2026
HomeKetareShugaban kasar Togo Faure Gnassingbé ya kori sojoji 559 na kasar daga...

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé ya kori sojoji 559 na kasar daga aiki

Sojoji 559 ne shugaban kasar Togo ya dauki matakin kora daga aikin sojan

A cewar majiyar hukumomin kasar wannan mataki ya biyo bayan kauracewa wajen aiki da wadannan sojoji suka yi na tsawon lokaci ba tare da wata hujja ba

Takardar sunayen sojojin da matakin ya shafa tuni aka mika ta ga babban hafsan tsaron kasar janar Dimini Allahare domin aiwatar da matakin nan take

Wannan mataki a cewar hukumomin Togon na da manufar karfafa da’a da ladabi a cikin rundunar sojin kasar da kuma tsabtace adadin dakarun

Kazalika hukumomin sun ce zai kara tunatar da alkawalin bada kai domin yin aiki da ake dauka musamman a irin wannan lokaci da yankin kasashen ke fama da matsalar tsaro

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata