Wasu ‘yan majalisar wakilai uku daga jam’iyyar PDP sun koma APC a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Laraba, suna zargin rikicin cikin gida da rashin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Wadanda suka sauya sheka su ne: Sanata Taofeek Ajilesoro, da Sanata Emmanuel Olusanya daga Jihar Osun sai Sanata Marcus Onobun daga jihar Osun Jihar Edo.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ambato mambobin na cewa sun dauki matakin ne domin hada kai da Shugaba Tinubu wajen cika alkawuran dimokuradiyya ga mazabunsu.
Wannan na zuwa a lokacin da PDP ke fuskantar matsin lamba, yayin da APC ke kara samun rinjaye a majalisar wakilai da ta dattawa.



