Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya rage farashin litar fetur karo na biyu a cikin mako guda.
Kamfanin man ya saukar da farashin litar fetur din daga N895 zuwa N890, wanda ke nuna ragin Naira 5 a kowace lita.
Gidajen mai na kamfanin NNPCL da ke kan hanyar Kubwa Expressway, Gwarimpa, Wuse Zone 4 da wasu sassa na birnin Abuja duk sun mayar da sabon farashin.