Ƙungiyar Super Falcons ta Najeriya za ta kara da ƙasar Maroko a wasan ƙarshe na Kofin Mata na Afirka (WAFCON) 2024 da za a fafata ranar Asabar, 26 ga Yuli, 2025. Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ke fatan lashe kofinta na 10 a tarihin gasar.
Najeriya ta riga ta lashe kofin sau tara, kuma ta doke dukkan wasannin karshe da ta buga a baya, sai dai ta gaza samun kofin ne kawai a shekarun 2008, 2012 da 2020.
A bangaren, tawagar mata ta kasar Maroko mai masaukin baki a bana, itama na fatan daukar kofinta na farko, bayan da ta sha kashi a wasan kusa da na karshe a 2022 hannun Najeriya da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Super Falcons sun doke Afirka ta Kudu 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Maroko ta lallasa Ghana a bugun fenariti 4-2 bayan wasan ya tashi 1-1.
Za a fafata wasan ne a filin Stade Olympique da ke Rabat, kuma dukkanin kasashen biyu sun nuna jajircewa wajen neman nasara a wannan gasa ta mata mafi girma a Afirka.