DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rikakken dan bindiga ‘Dan Dari Biyar’ ya bakuncin lahira hannun sojojin Nijeriya a Sokoto

-

Dakarun sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation FANSAN YANMA sun kawo kashen fitaccen shugaban ƴan bindiga da aka fi sani da Dan Dari Biyar a wani samame da suka kai a yammacin ƙaramar hukumar Sabon Birni, Jihar Sokoto.

Wata majiya mai karfi daga rundunar sojin ƙasa ta tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa an yi ajalin shugaban ƴan ta’addan ne ranar Alhamis a cikin dajin dake tsakanin Turtsawa, Mazau da Zango, lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kudin fansa daga iyalan waɗanda suka sace.

Google search engine

Majiyar ta bayyana cewa Dan Dari Biyar yana da mugun hali, inda ke azabtar da waɗanda aka sace kafin ya nemi kuɗi masu yawa.

Rahoton jaridar Daily Nigerian yace an kuma gano makamai, harsasai da na’urorin sadarwa daga wajen harin, yayin da sojoji ke ci gaba da bin sahun ragowar ‘yan ƙungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 bisa zarginsu da satar jarrabawa

Jami'ar tarayya da ke jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 daga karatu bisa samunsu da laifin satar jarabawa. Rahotanni sun...

Mafi Shahara