Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron koli na Majalisar Ɗinkin Duniya kan tsarin abinci (UNFSS+4) da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.
A jawabin da ya gabatar a madadin shugaban ƙasa, Shettima ya bayyana cewa taron na da nufin samar da makoma mai ɗorewa wadda ke ginuwa kan yalwa, daidaito da mutuncin ɗan’adam.
Ya ce Afirka na buƙatar tallafin kuɗi mai sauƙi kuma tabbatacce don zuba jari a harkar noma, inganta karkara, ilimi da ababen more rayuwa, tare da buƙatar daidaita kuɗaɗen sauyin yanayi da tsarin abinci.
Ya ƙara da cewa Najeriya na ƙara ƙaimi a bangaren noma ta amfani da fasahar zamani irin su Artificial Intelligence (AI), geospatial analytics, da bayanan tauraron dan adam domin magance ƙarancin abinci a ƙasar.



