DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An ceto matashi da ran sa bayan shafe sa’o’i 10 acikin baraguzan gini a Abuja

-

Wani matashi dan shekaru 27 daga Jamhuriyar Nijar, Aliyu Salisu, an ceto shi da ransa bayan shafe kusan sa’o’i 10 a cikin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya rushe a unguwar Lifecamp da ke Abuja.

Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh, ta fitar ranar Lahadi.

Google search engine

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 6:15 na yamma a ranar Asabar, inda aka samu kiran gaggawa. DPO na yankin Lifecamp ya gaggauta daukar mataki, ya tare wajen da lamarin ya faru tare da hadin gwiwar hukumomin ceto.

A cewar Adeh, da misalin karfe 4:00 na asuba ranar Lahadi, an ceto Aliyu Salisu da ransa daga cikin baraguzan ginin sannan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Cedar Crest da ke Gudu domin kulawa da lafiyarsa.

Kwamishinan ’yan sanda na FCT, Ajao Adewale, ya yaba da jajircewa da hadin gwiwar jami’an ceto da mazauna yankin wajen ceto rayuwar matashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 bisa zarginsu da satar jarrabawa

Jami'ar tarayya da ke jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 daga karatu bisa samunsu da laifin satar jarabawa. Rahotanni sun...

Mafi Shahara