Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ya bukaci ’yan siyasar Arewa da su goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin samun wa’adi na biyu a zaben 2027.
Gbajabiamila ya yi wannan kiran ne a yayin taron tattaunawa na 2025 da kungiyar tsoffin ’yan majalisa na kasa reshen Arewa ta shirya a birnin Abuja. Ya ce Tinubu shugaba ne da ya cancanci cikakken goyon baya duba da tarihin aikinsa da jajircewarsa ga hadin kan kasa.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Tinubu da Bago domin sake tsayawa takara a 2027.



