DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ka daina dogaro da gwamnoni, ka Jagoranci tallafa wa talakawa da kanka – Femi Falana ga Shugaba Tinubu

-

Fitaccen lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki jagoranci kai tsaye wajen yaki da talauci, maimakon barin lamarin hannun gwamnoni.

Gidan talabijin na Channels ya ambato wata sanarwa da ya fitar, inda ya soki kalaman Tinubu a taron gwamnonin APC inda shugaban ya bukaci su “ji Ć™asa” wajen saukaka wa talakawa.

Google search engine

Falana ya ce gwamnati ya kamata ta tabbatar da aiwatar da dokar Hukumar Shirin Tallafi ta Kasa (NSIPA) a matakin jihohi 36.

Ya kuma soki yadda gwamnatin tarayya ke kashe makudan kudade kan gyaran gine-gine, yayin da aka ware Naira biliyan 32.7 kacal ga shirye-shiryen rage talauci, sabanin N39bn da aka kashe kan gyaran cibiyar taro ta kasa a Abuja.

Falana ya nemi a mayar da hankali kan shirye-shiryen N-Power, ciyar da ɗalibai, bayar da rance mai sauƙi da tallafin kuɗi ga talakawa, domin rage radadin talauci da matsin rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara