‘Yan bindigar da suka kai hari a akalla garuruwa 16 tsakanin Asabar da Lahadi, a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara sun yi aja mutane 5 tare da yin garkuwa da mata da dama.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa a ranar Asabar, ‘yan bindigar sun farmaki garuruwa 8 ciki har da Dan Isa, Kyatawa, Tudu, Gidan Haruna, da sauransu, inda suka kashe mutum 1 a Gidan Haruna kuma suka sace mata 8.
A ranar Lahadi kuma, sun sake dawowa Kwalau inda suka kashe mutum 4 — Abubakar, Murtala, Aminu da Bello — tare da raunata wani Ashafa, wanda aka kai asibitin Kaura Namoda.
Rahotan jaridar Daily Trust ya ce ‘yan sa-kai sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar a daren Asabar, lamarin da ya sa suka ja da baya.
Sai dai, da safe sun dawo cikin shiri, inda suka kai farmaki wajen taron ‘yan sa-kai, inda suka kashe 4, suka raunata 1, tare da sace mata da kwashe kayan abinci da na gida.



