Home Labarai Matasa fiye da milyan 1 suka nemi shiga shirin N-Power a kwanaki...

Matasa fiye da milyan 1 suka nemi shiga shirin N-Power a kwanaki 2

102
0

Ma’aikatar kula da al’amuran jin kai da kuma kiyaye afkuwar bala’o’i ta ce ta karbi takardun neman shiga shirin Npower fiye da Miliyan daya daga sassa daban-daban a fadin kasar nan cikin kwanaki biyu.

Mataimakiyar darakta fannin yada labarai ta ma’aikatar Rhoda Ilya ta bayyana haka a wata sanarwa ta kuma ce adadin takardun neman shiga shirin yana nuni da yawan matasan da ke bukatar samun aikin yi da kuma yadda jama’a suka kara yin amanna da shirin.

Rhoda ta kara da cewa dukkan matasan kasar nan da ke tsakanin shekara 18 zuwa 30 da ke da shaidar kammala karatu dama wanda ba su da ita za su iya neman gurbin samun shiga shirin na Npower a fannin N-agro wanda zai ba da fifiko akan aikin gona.

Daga karshe ta ce za a yi adalci da yin gaskia wajen ba da gurabe a shirin tare da sanar da jama’a halin da ake ciki game da shirin na Npower.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here