A kalla mata da ‘yan mata 20 ne ‘yan bindiga suka sace a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, yayin da suke neman itace a wajen gari a ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin, Sufyanu Moriki, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, yana mai cewa har yanzu masu garkuwar ba su nemi kudin fansa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya ce hukumar su ba ta samu bayani kan lamarin ba tukuna.
Rahotanni sun bayyana cewa hadin gwiwar ‘yan ta’adda da mayaka ma su da’awar jihadi na kungiyar Lakurawa a yankin na kara dagula lamarin tsaro a Arewacin Najeriya.



