https://punchng.com/minister-says-no-automatic-ticket-for-apc-defectors/
Ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Chief Uche Nnaji, ya gargadi masu niyyar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a Jihar Enugu da su daina tunanin samun tikitin takara kai tsaye ko kwace shugabancin jam’iyyar.
Yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Enugu ranar Asabar, Nnaji ya ce za a karbi masu sauya sheka amma kowa zai bi hanyar zaben fidda gwani. Ya ce wasu ‘yan siyasa da suka rasa matsayi na yawo a Abuja suna shirin shiga APC ta bayan gida domin kwace ikon ta.
Ya kuma yi nuni da rade-radin cewa Gwamna Peter Mbah na iya shiga jam’iyyar, abin da ke tayar da hankalin wasu mambobi, inda ya jaddada cewa babu tikitin kai tsaye ga kowa.