’Yan damben Japan, Shigetoshi Kotari da Hiromasa Urakawa, duk masu shekaru 28, sun rasu bayan samun mummunan raunin kwakwalwa a fafatawa daban-daban da aka gudanar a Korakuen Hall, Tokyo, ranar 2 ga Agusta.
Rahoton Channels TV ya ce Kotari ya fadi bayan kammala zagaye na 12 da Yamato Hata, inda ya rasu a ranar 8 ga Agusta sakamakon acute subdural haematoma.
Urakawa kuwa, wanda aka dakatar a zagaye na takwas da Yoji Saito, ya rasu bayan kwana biyu.
Hukumomi sun ce wannan na iya zama karo na farko a Japan da ’yan dambe biyu a cikin gasa guda suka bukaci tiyata a kwakwalwa.



