DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya na ganawar sirri shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Ngozi Okonjo-Iweala a fadarsa dake Villa a Abuja

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya karɓi bakuncin Ngozi Okonjo-Iweala a Fadarsa dake Abuja a ranar Alhamis.

Tinubu da Okonjo-Iweala sun shiga tattauna kan batutuwan cinikayya masu muhimmanci ga ƙasa da nahiyar Afrika da ma duniya baki ɗaya.

Google search engine

Tattaunawar shugaba Tinubu da Okonjo-Iweala ya zo ne makonni biyu kafin karewar wa’adinta na farko a ranar 31 ga watan Agustan nan na 2025, kafin ta fara wa’adinta na biyu a ranar 1 ga Satumba, 2025.

Okonjo-Iweala ta kafa tarihi a shekarar 2021 a matsayin ‘yar Afirka ta farko kuma mace ta farko da ta shugabanci Kungiyar ta kasuwanci ta Duniya WTO.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Mafi Shahara