Wata uwa a jihar Katsina mai suna Zahara’u Abdulsalam da ke zaune a kauyen Falale a karamar hukumar Jibia, ta bayyana ma DCL Hausa yadda ciwon yunwa ya yi ajalin yarinyarta sakamakon hare-hare yan bindiga a yankin.
Zahara’u ta ce rashin karancin ruwan nonon ne ya zamo silar mutuwar yarinyarta amma ta alakanta hakan da yadda barayin daji suka addabi yankin nasu.
“Sanadiyyar lalacewar rayuwarmu, barayin daji ne, suka kore mamu dabbobi suka bar mu haka nan” in ji Zahara’u
“Yunwa ce sanadin mutuwar diyata, sakamakon ni ban koshi ba, babu ruwan nono a jikina, sai na fara ba ta abinci kuma ba ta isa cin abinci ba, daga nan sai ciwon yunwa ya kamata” Zahara’u ta shaida wa DCL Hausa cikin fushi.
A karshen watan Yulin da ya gabata ne kungiyar likitoci ta MSF ta ce kananan yara sama da 600 ne suka mutu a jihar Katsina a sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki.
A cikin makon nan gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da kwamiti na musamman da zai tsara yadda za ta magance matsalar abincin mai gina a tsakanin kananan yaran jihar. Gwamnan jihar Dikko Umaru Radda, PhD, ya ce “mun san akwai matsalar ba za mu kauce mata ba, za mu dauki mataki.”