DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutane 62 da aka sace sun kubuta bayan luguden wuta kan sansanin yan bindiga a Katsina

-

Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutum 62 da aka yi garkuwa da su sun kubuta, biyo bayan luguden wuta da rundunar sojin sama ta kai a sansanin fitaccen jagoran yan bindiga Muhammadu Fulani, a karamar hukumar Dan-Musa.

Kwamishinan tsaro na cikin gida Dr Nasir Mu’azu ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa luguden wutar sojin saman ya kai ga yankin Jigawa Sawai, da ke kan iyakar Katsina da Zamfara

Dr Nasir Mu’azu yace daga cikin mutanen da suka kubuta, mutum 12 suna samun kulawar likitoci a Asibitin Gwamnati dake Matazu, yayin da wasu 16 ke tare da sojojin Najeriya a Kaiga Malamai.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Atiku Abubakar da Babachir Lawal mambobin bogi ne – ADC ta Adamawa

Jam'iyyar hadaka ta ADC reshen jihar Adamawa ta bayyana tsohon shugaban Nijeriya Atiku Abubakar da tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Babachir Lawal a matsayin mambobin bogi. Shugaban...

Real Madrid za ta bayar da aron dan wasan gaba Endrick

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana shirin bayar da aron matashin dan wasanta na gaba Endrick.   Jaridar Punch ta ruwaito cewa tuni Real Madrid...

Mafi Shahara