DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’an tsaro sun kama tsigaggen shugaban Korea ta Kudu

-

Jami’an tsaro a kasar Korea ta Kudu , sun kama tsigaggen shugaban kasar Yoon Suk Yeol bayan da suka kutsa inda ya samu mafaka tare da kama shi.
Kamawar ta shi ta sa ya zama shugaban kasar na farko da ke kan mulki da Jami’an tsaro masu bincike na musamman suka kama.
Shugaba Yoon, mai shekaru 64 ana binciken sa ne akan saka dokar ta baci mai cike da sarkakiya a ranar 3 ga watan Disambar da ta gabata 2024, abinda ya jefa kasar cikin mummunan rikici na bore.
Kamun na shugaba Yoon, ya kawo karshen wasan buya tsakanin shugaban da Jami’an tsaron sa da na masu bincike na musamman.
Sai dai duk da tsige shugaban da Majalisar kasar tayi shugaban na cigaba da rike iko har sai Kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da tsige shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara