Babban Hafsan tsaron Nijeriya CDS, Janar Christopher Musa, ya ce nan ba da jimawa ba za a bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.
Janar Musa ya bayyana haka ne a daren Alhamis lokacin da yake tattaunawa a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Ya ce ana ci gaba da aiki da zakulo masu daukar nauyin ta’addanci, sai dai jinkiri ya shiga lamarin saboda al’amuran shari’a da kuma alakar da take da wasu kasashen waje.
Ya ce wasu daga cikinsu suna da kudade daga kasashen waje, don haka dole ne abi ta hanyar doka,kazalika akwai wadanda suke a cikin gida Nijeriya.
CDS ya kuma yabawa hukumar binciken bayanai na kudi NFIU, bisa rawar da take takawa wajen gano hanyar kudaden da ake amfani da su don daukar nauyin ta’addanci, inda ya ce dama an riga an samu nasarori da kama wasu mutane.



