Wasu tarin magoya bayan jam’iyyar APC a karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto sun fice daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar ADC, inda suka danganta hakan da rashin gamsuwa da yadda jam’iyyar mai mulki ke gudanar da al’amuranta a jihar.
An karɓi waɗanda suka sauya sheƙar ne a hukumance daga hannun Sanata Abubakar Gada, wanda ya bayyana wannan ci gaban a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin kafa haɗin gwiwa mai faɗi domin ceto jihar Sokoto da kasa baki ɗaya daga abin da ya kira gazawar mulki.
Da yake jawabi a wajen taron tarbar sababbin mambobin, Sanata Gada ya ce yawan rashin jin daɗi da jagorancin APC ya sanya mutane da dama shiga jam’iyyar ADC domin neman samun sauyi mai ma’ana.