DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban Sashen Hausa na BBC Aliyu Tanko ya ajiye aiki

-

Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ajiye aikinsa bayan ya shafe shekaru 17 yana aiki da gidan. Tanko, wanda ya zama babban editan BBC Hausa a 2019, ya tabbatar wa DCL Hausa cewa ya mika takardar murabus dinsa a ranar Alhamis tare da mika ragamar aiki ga wani jami’in BBC.

Rahotanni sun nuna cewa ajiye aikin nasa ya zo ne daidai lokacin da ake rade-radin cewa BBC ta dakatar da shi tare da kaddamar da bincike kan zargin kuntata wa wata tsohuwar ma’aikaciya. Tanko dai ya ki yin karin bayani kan wannan batu, sai dai a makonnin da suka gabata wata tsohuwar ma’aikaciyar BBC, wadda yanzu ke aiki a TRT Hausa, ta yi zargin cewa wani shugabanta a BBC ya zalunce ta a lokacin da take aiki da BBC. Duk da ‘yar jaridar ba ta ambaci sunansa ba, amma an rika yada jita-jitar shi ne take zargi.  

Google search engine

A matsayinsa na shugaban BBC Hausa, Aliyu Tanko ya jagoranci ’yan jarida sama da 40 da ke aiki a Landan, Abuja da kasashe makwabta, ya kula da shirye-shiryen rediyo hudu a rana, sa’o’i 20 na labaran dijital, da kuma rahoton talabijin a kowace rana daga Litinin zuwa Juma’ai. Haka kuma, a karkashin jagorancinsa BBC Hausa ta samu kirkiro shirye-shirye kamar su Daga Bakin Mai Ita, Ku San Malamanku, Zamantakewa da Korona Ina Mafita.

Tun daga shekarar 2013, Aliyu Tanko ya bayar da gudunmawa wajen canza fuskar kafafen dijital na BBC Hausa a matsayinsa na editan dijital na farko, abin da ya sa aka yaba masa a hukumance. Ya kuma taimaka wajen kaddamar da sabbin harsunan BBC Pidgin, Igbo da Yoruba a 2017, inda ya jagoranci sabbin ma’aikata 50 tare da horas da su kan amfani da kafafen zamani.

BBC Hausa dai ita ce babban sashe cikin harsunan Afirka, inda take samun masu sauraro sama da miliyan 23 a kowane mako ta rediyo, da miliyan 10 masu ziyartar shafin intanet. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hadimin Gwamna Abba Gida-Gida ya maka Jaafar Jaafar a kotu kan zargin sa da badakalar 6.5B

Hadimin gwamnan Kano Abdullahi Rogo ya maka mawallafim Jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar a kotu bisa wallafa labarin zargin almundahanar naira biliyan 6.5 Rogo na son...

Yadda na rasa ɗiyata da jikokina sanadiyyar shan ‘Dettol’ a matsayin magani

Rashin sani ya haddasa mutuwar yata da jikokina bayan da suka sha Dettol a matsayin magani Wata dattijuwa mai suna Asiya Hassan da ke zaune a...

Mafi Shahara