DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Na goyi bayan tikitin Muslim-Muslim ne a 2023 don manufar siyasa ba addini ba – Elrufa’i

-

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa goyon bayansa ga tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa na 2023 ba don addini ba ne, illa siyasa ce kawai domin samun nasara.

El-Rufai ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Channels ta cikin shirin Sunday Politics, inda ya ce matakin na jam’iyyar APC wani tsari ne na siyasa da aka yi tunani akai domin samun nasara a zabe, ba wai wani abu da ya shafi addini ba.

Google search engine

A cewarsa dama tsarin na siyasa ne, kuma dabarar lashe zabe ce, ba wani batu na addini ba,idan kana neman cin zabe kana duba dukkan dabarun da za su baka nasara.

Ya ce, irin wannan tunani shi ma ya yi lokacin da ya tsaya takarar gwamna a Kaduna a kan tikitin Musulmi da Musulmi, kuma hakan bai tauye wa Kiristoci hakkin su ba,kuma duk shugaban da yake son samun nasara ba zai takaita kansa ga addini ko kabila daya ba dole ne ya nemi mutane ko ta ina ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara