Gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai gargadi tana zarginsa da shirin tayar da hankalin jihar a ƙarƙashin mulkin Gwamna Uba Sani.
A cikin wata hira da aka yi da El-rufa’i a cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya da ta Kaduna sun biya ’yan bindiga makudan kudade a matsayin wani ɓangare na bin matakin sulhu da ake ɗauka don kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Sai dai Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya musanta wannan ikirari a ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna, Suleiman Shuaibu, ya sanya wa hannu, gwamnatin jihar ta ce ba za ta zura ido ta bari tsohon gwamnan, wanda ta zarga da barin jihar cikin hali na tabarbarewa, ya jawo rikice-rikice da tayar da tarzoma ba.
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta ga dole ta yi wannan gargaɗi na ƙarshe ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wanda ta zarga da ƙoƙarin haifar da rikici a jihar, da nufin dagula lamurra da maida Kaduna zuwa tsohon yanayi na rikicin kabilanci da addini, rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki.




Wannan duk Hauragiya ce Gwamnatin Kaduna take yi da kuma Tarayya, mu Talakawa muna mun zura musu Ido suyi su gama. Mu fatanmu shi ne Ubangiji Allah ya nuna mana 2027 lfy. Za su kwashi Zubin Adashen da suka yi