A cikin wani kudurin doka ne da ya saka wa hannu shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar ABDOURAHAMANE Tiani ya sanar da nada malan Ibrahim Manzo Djallo shugaban rukunin mujallar Aïr Info da gidan radiyon Sahara a matsayin wanda zai jagoranci hukumar sanya ido kan kafafen yada labarai ta kasar Nijar wato l’ Observatoire National de Communication ONC a takaice.
Daman dai an jima kungiyoyin ‘yan jarida da na ‘yan fafitika a Nijar na kiraye kirayen gwamnatin mulkin sojan kasar da ta girka wannan hukuma domin magance irin matsalolin da ake samu tsakanin gwamnatin da wadansu kafafen yada labaran.
A baya dai tun kafin juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023 akwai makamanciyar wannan hukuma da ake kira Conseil Supérieur de la Communication CSC to amma sojojin suka rusa ta



