Shahararren dan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa bai taɓa dogaro da kuɗin iyayensa wajen gina harkokin kasuwancinsa ba.
A wata tattaunawa da Bloomberg ta yi da shi tun a shekarar 2020, wadda aka wallafa a yanar gizo, Dangote ya ce kakansa Alhassan Dantata, shi ne mafi arziki a yammacin Afirka tun a shekarun 1940, haka nan mahaifinsa ma ya kasance ɗan kasuwa mai kuɗi kuma ɗan siyasa.
Sai dai ya ce dukiya ko kadarorin da ya gada daga wurin mahaifinsa ya mika su ne wajen ayyukan alheri.
Dangote ya bayyana cewa ya fara sana’ar sayar da siminti a Legas kafin daga baya ya zuba jari sosai a masana’antar siminti wadda a wancan lokaci aka fi dogaro da shigo da shi daga ƙasashen waje.
Dangote ya kafa Dangote Group, wadda ke da rassa sama da 15 a ƙasashe akalla 10 na Afirka, ciki har da siminti, sukari, man fetur, taki, da fitar da kayayyakin sufuri da gine-gine.



