Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i bacin ransa kan abin da ya Kira da tauye hakkin da kundin tsarin mulki bayar, bayan da rundunar’ yan sanda ta hana gudanar da taron jam’iyyar ADC a jihar.
Kalaman nasa sun biyo bayan da wasu bata gari suka tarwatsa taron kwamitin jam’iyyar a makon da ya gabata, lamarin da ya bayyana a matsayin rashin doka da oda, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kaduna, Elrufa’i ya ce sun yi niyyar gudanar da taron ne da nufin jajantawa mambobin jam’iyyar da aka kai wa farmaki.
Sai dai hakan bai samu ba, sakamakon wasikar da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya aike musu na dakatar da taron.



