Hukumar zaben Nijeriya INEC ta amince da shugabancin jam’iyyar ADC karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar Dattawa, David Mark.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hukumar ta tabbatar da sabon tsarin ne bayan wani lokaci da sake shugabancin jam’iyyar.
Shugabannin da aka amince da su sun haɗa da David Mark a matsayin shugaban ta riko na ƙasa, Ogbeni Rauf Aregbesola kuma sakataren ta na ƙasa, Dr. Ibrahim Mani ma’ajin jam’iyyar, sai Akibu Dalhatu sakataren kuɗi.
Bayan wannan sahalewa, ana sa ran ADC za ta fara shirin tunkarar zaben 2027 ta hanyar ƙarfafa tsarin jam’iyyar a fadin ƙasar.



