Mai horas da tawagar Super Eagles, Eric Chelle, ya ce duk da wahalar da ake ciki a rukuninsu, Nijeriya ba ta daina burin zuwa gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 ba.
Nijeriya ta tashi canjaras 1-1 da Afirka ta Kudu, abin da ya bar ta a matsayi na uku da maki 11 daga wasanni 8, yayin da Bafana Bafana masu jan ragamar rukunin C suke da maki 17.
Chelle ya yaba wa kwazon ’yan wasansa duk da rashin samun nasarar da ake bukata, inda ya ce sun yi iya kokarinsu, amma Afirka ta Kudu kungiya ce mai karfi, kuma suna da gogaggun ‘yan wasa.
Nijeriya dai na neman cin nasara a wasanninta biyu na karshe domin samun damar zuwa gasar kai tsaye.



