DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sandan Kebbi sun kama mutum shida kan zargin satar zinare mai kimar Naira miliyan 109.5

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a satar zinare da kimar sa ta kai Naira miliyan 109.5 a garin Ka’oje, karamar hukumar Bagudo.

Mai magana da yawun rundunar, Nafiu Abubakar, ya ce an shigar da korafi ranar 4 ga Satumban 2025 a sashen bincike na SCID, Birnin Kebbi, wanda ya kai ga gano cewa wani jami’in hukumar gyaran hali, Ibrahim Abubakar ne ya saci kayan.

Google search engine

Rahoton ya ce Abubakar ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa ya sayar da kayan ga wasu dillalai daga Sokoto da Kebbi, ciki har da Sa’adu Ibrahim Darhami, Hamza Ahmad, Nasiru Sani, da Tasi’u Umar.

Bincike ya kuma nuna cewa wani Ibrahim Usman Oroji ya taimaka wajen rarraba kayan, inda ya karɓi naira miliyan 2.5 a matsayin rabonsa.

Haka kuma, wani Mustapha Hassan ya taimaka wajen boye kudin ta hanyar sayen filaye biyu a Birnin Kebbi.

Daga cikin abubuwan da aka kwato akwai zoben zinare biyu, babur kirar Haojue, wayoyi samfurin iPhone da Samsung.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara