Kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilan Najeriya ya yi zama da ministan kuɗi Wale Edun, da na tsare-tsare da kasafin kuɗi, Sanata Atiku Bagudu, kan jinkirin aiwatar da kasafin shekarar 2024/2025.
Shugaban kwamitin, Abubakar Kabir Bichi, ya ce ’yan Nijeriya na nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da kasafin, don haka majalisa ta yi kira da a hanzarta aiki a kai.
Ministan kuɗi, Wale Edun, ya bayyana cewa zuwa watan Satumba 2025, an aiwatar da kashi 80 cikin 100 na kasafin 2024, yayin da majalisar ta tsawaita wa’adin kasafin har zuwa Disamba.
Ya ce an fi mayar da hankali kan ayyukan da ke zuwa kai tsaye ga al’umma, kamar hanyoyi da sauran muhimman ayyuka.
Shi ma Ministan tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya yaba wa majalisar bisa goyon baya ga sauye-sauyen gwamnati, musamman na haraji, tare da cewa akwai ci gaba amma akwai sauran gyare-gyare da za a gudanar.



