Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin dakatar da Kwamishinan Lafiya na jihar, Kwamared Yunusa Isma’il, daga mukaminsa nan take har zuwa wani lokaci.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya fitar a yau Alhamis a Birnin Kebbi, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa zargin sakaci da yin watsi da aikinsa.
A cewar sanarwar, Gwamna Idris ya umarci Kwamishinan da aka dakatar ya bayar da cikakken bayani kan dalilin da zai sa kada a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.
Hakan, a cewar gwamnatin jihar, ya biyo bayan raina aikinsa da kuma rashin mutunta amanar da aka ɗora masa a matsayin Kwamishinan Lafiya.



