Rahoton gidan talabijin na Channels ya nuna cewa, kwana biyu kacal da kungiyar masu dakon man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ta dakatar da yajin aikin ta, kungiyar ta sake Zargin hukumar kamfanin Dangote Refinery da karya yarjejeniyar da aka cimma.
A cikin wata sanarwa da Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, tare da Sakataren Janar, Afolabi Olawale suka rattaba wa hannu, kungiyar ta gargadi cewa za ta iya sake komawa yajin aikin da aka dakatar, saboda karya matsayar da aka cimma tsakanin Dangote Refinery, gwamnatin tarayya da direbobin manyan motoci da ke karkashin kungiyar NUPENG-PTD.
Sai dai duk da wannan matsayi da aka rattaba hannu a ofishin DSS, a jiya an umarci direbobin manyan motoci da ke cikin NUPENG-PTD da su cire tambarin kungiyar daga motocinsu.



