Tsohon kyaftin din Super Eagles kuma mai tsaron ragar Nijeriya, Vincent Enyeama, ya bayyana cewa yana da shirin bayar da gudummawarsa ga tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya kyauta ba tare da ko sisi ba, idan har za a ba shi dama.
Enyeama ya yi wannan furuci ne a tattaunawa da kafar Twitter Space a karshen makon da ya gabata.
Ya ce yana sha’awar ganin an samu ci-gaba a kwallon kafar Nijeriya musamman a bangaren masu tsaron raga, dalili kenan da ya sa shi yanke wannan shawara.
Enyeama ya ce ko a Faransa yana horar da ƙananan masu tsaron raga ba tare da karɓar kuɗi ba, kuma zai iya yin haka a Nijeriya, abinda zai buƙata kawai shi ne hukumar NFF ta ɗauki nauyin tafiye-tafiyen da zai yi tare da masaukin da zai zauna.



