Gwamnatin Jihar Kebbi ta musanta zarge-zargen da tsohon ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya yi kan Gwamnan jihar Nasir Idris, Kauran Gwandu.
Malami, wanda shi ne jagoran jam’iyyar ADC a jihar, ya rubuta wata takarda inda ya yi zargin cewa gwamnan na da hannu wajen shigo da ’yan daba daga waje da kuma safarar makamai a boye.
Sai dai a wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki ya fitar, gwamnatin ta ce wannan zargi ba gaskiya bane, yunƙuri ne kawai na bata sunan gwamnan.
Sanarwar ta ce abin takaici ne cewa Malami, wanda ya rike mukaman gwamnati na kasa, ya ƙirƙiro irin waɗannan zarge-zargen marasa tushe ba tare da gabatar da hujja ba.
Ta ce idan har abinda Malami ke fada gaskiya ne ya fito ya bayyanawa jama’a da kuma hukumomin tsaro.



