Ma’aikatar ilimi ta Najeriya ta bayyana cewa wajibi ne kowane malamin makaranta ya yi rajista da hukumar bayar da shaidar malunta TRCN kafin shiga aji ya koyar a fadin kasar.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce hakan na daga cikin yunkurin tabbatar da sauyi mai inganci a tsarin koyar da dalibai a fadin Najeriya.
Wannan ya zo bayan da a ranar Alhamis 11 ga watan Satumba, ministan ilimi Dr. Tunji Alausa yayi gargadin cewa wajibi ne ya kasance dukkanin malamai makarantun sakandiren da ke fadin kasar sun cancanci koyarwa ta hanyoyin da suka dace.



