Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta bayyana cewa daga ranar Litinin zuwa Laraba za a samu ruwan sama tare da guguwa da tsawa a sassa daban-daban na ƙasar.
An yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa musamman Adamawa, Taraba da Gombe.
Kazalika za’a samu ruwan sama kadan-kadan a garuruwan da ke yankin kudu a cewar hasashen na hukumar ta kula da yanayi a Najeriya.
NiMet ta shawarci jama’a, musamman direbobi da manoma da su dauki matakan kariya domin kauce wa hadura yayin da ake sa ran ruwan sama mai yawa.