Rahotanni daga ƙauyen Galumji da ke ƙaramar hukumar Dukku a jihar Gombe, sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun halaka wani mutum mai suna Hammayidi duk da cewa danginsa sun biya su naira miliyan biyar 5, kudin fansa.
An sace Hammayidi daga gidansa cikin dare kimanin makonni uku da suka wuce, sai dai duk da biyan kudin, an gano gawarsa da ta fara ruɓewa a ƙarƙashin gada a dajin da ke tsakanin Dukku da Akko.
Daily Trust ta rawaito cewa wani ɗan’uwansa ya bayyana cewa an daure shi,daga bisani aka yanka sannan aka harbe shi.
Sun ce sun tara kudin fansar ne ta hanyar sayar da amfanin gona da kuma dabbobinsu a kasuwar Dukku.
Bayan satar Hammayidi, ‘yan bindigar sun sake kai farmaki gidaje biyu a yankin, inda suka sace shanu biyu, sannan daga baya suka yi ƙoƙarin sace wani makwabcinsa wanda ya tsere, amma matarsa tana hannunsu har zuwa wannan lokaci.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoton,an yi ƙoƙarin samun rundunar ‘yan sandan jihar Gombe amma ba a samu ba domin mai magana da yawunsu DSP Buhari Abdullahi, bai amsa kiran waya ba.



