Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wata mota dauke da bindigogi a kan hanyar Gummi zuwa Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane, ƙarƙashin jagorancin ASP Bilyamin Koko, sun tsayar da wata Toyota Corolla a ƙauyen Gambanda Godabe, inda suka gano makaman da aka ɓoye a cikin jaka da aka saka lemon tsami a samanta.
Bincike ya nuna cewa makaman sun haɗa da bindigogi AK-47 guda huɗu, harsasai 228.
Wanda ake zargi, mai suna Nasuru Dawan Jiya, ya amsa cewa yana jigilar makaman ne zuwa ga ‘yan bindigar da ke a ƙauyen Gurusu.



