Tawagar kwallon kafar Najeriya Super Eagles ta sauka da maki daya a kan jadawalin FIFA, inda ta koma ta 45 a duniya.
Matakin da ke kunshe a wallafar da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi a shafinta na X, ya nuna cewa Najeriya na kan matakinta a nahiyar Afirka na kasancewa kasa ta 6.
Wannan ya biyo bayan saukar da tawagar ta samu a jadawalin baya, inda da koma ta 44 daga ta 43 a watan Agustan da ya gabata, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
A halin yanzu dai kasashe na ci gaba da fafatawa a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.



