Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta kammala dukkanin ayyukan da ke gabanta ba tare da ciyo bashin ko sisin-kobo ba.
Gwamnan ya sha wannan alwashi ne yayin kaddamar da wani titi a karamar hukumar Lere, inda ya ce za su kammala har da ragowar ayyukan da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.
A cewar sa, tuni suka kammala wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin da ta gabata ta faro musamman a karamar hukumar ta Lere, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.



