DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da mai ga ‘yan kasuwar da ba su da rijista

-

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da man fetur kai tsaye ga ‘yan kasuwar da basu da rijista daga ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.

Wannan sanarwar ta fito ne daga sashen gudanarwar kasuwanci na kamfanin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Google search engine

Matatar ta Dangote ta ce matakin ya yi daidai da shirin su na Free Delivery Scheme, wato kai man kai tsaye zuwa tashoshin sayarwa, tare da hana dillalai marasa rijista cinikin kai tsaye ko kuma ta hannun wasu.

Sanarwar ta kuma ja hankalin ‘yan kasuwa cewa duk wani biyan kudi da za a yi bayan ranar 18 ga Satumba ba za a karɓa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara