Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa kusan mutane biliyan 1 ne ke fama da matsalar lafiyar tunani, inda ta yi kira ga gwamnatoci su dauki matakan magance matsalar.
Shugaban hukumar Dr. Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana haka gabanin wani muhimmin taro kan cutuka marasa yaduwa, da kuma lafiyar tunani, wanda za a gudanar a ranar 25 ga watan Satumban 2025.
A cewar sa, rashin daukar mataki daga masu ruwa da tsaki ka iya janyo asarar miliyoyin rayuka da kuma dakile ci gaba ta fuskar tattalin arziki, kamar yadda Channels TV ya wallafa.



