DCL Hausa Radio
Kaitsaye

APC da jam’iyyun adawa sun bayyana abinda suke sa rai ga sabon shugaban INEC

-

Yayin da wa’adin shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ke gab da karewa a watan Nuwamba, manyan jam’iyyun siyasa sun bayyana bukatunsu daga wanda zai gaje shi kafin babban zaben 2027.

Jam’iyyar APC ta ce tana bukatar shugaban da zai bai wa kowa da kowa dama iri tare da gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Google search engine

Ita kuwa PDP ta jaddada cewa sabon shugaban dole ne ya zama mutum mai gaskiya, tsantseni da cikakken ’yancin da gwamnati ba za ta yi amfani da shi ba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana cewa dole ne shugaban INEC ya kasance mai tsantsar gaskiya kuma ya cika shekaru 50 zuwa sama, sa’annan kafin nadin shugaban kasa, dole ne sai majalisar dattawa ta tabbatar da shi.

Tuni rahotanni suka ce shugaba Tinubu ya fitar da jerin sunayen mutanen da za su iya zama shugaban hukumar, yayin da jam’iyyun adawa ke gargadin zabo shugaban marar inganci, zai iya shafar sahihancin a zaben shekarar 2027 mai zuwa a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara