Dan siyasa kuma lauya a Nijeriya, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, na da damar neman hakkinsa a kotu kan watanni shida da ya rasa a matsayinsa na gwamna, sakamakon dokar ta baci da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a jihar.
Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels,inda ya ce gwamnan bai kamata ya sauka daga mulki a ranar 29 ga Mayu, 2027 ba, saboda hakan zai rage masa wa’adin mulki da kundin tsarin mulki ya tanada.
A cewarsa bisa ga fassarar da kotun koli ta yi a baya, wa’adin mulkin gwamnoni na shekaru hudu abu ne da ba za a iya tauye wa ba.
Ya ce kundin tsarin mulki a sashi na 180(2) ya bayyana cewa wa’adin mulki na shekaru hudu ne, daga ranar da aka rantsar da gwamna,idan Fubara ya bar ofis a 29 ga Mayu, 2027, zai zama bai yi cikakkun shekaru hudunsa ba.
Okonkwo ya ce, lokacin da aka cire Fubara daga ofis na tsawon watanni shida, an tauye wa ‘yan jihar Rivers damar yin amfani da zabensu na shekaru hudu, saboda haka, a fahimtarsa, wa’adin Fubara ya kamata ya ƙare ne a 29 ga Nuwamba, 2027.



