Majalisar wakilan Nijeriya ta umurci Akanta Janar na kasa, Shamsudeen Ogunjimi, da ya gabatar da cikakkun bayanai kan yadda aka biya kuɗaɗen kwangila na sama da naira tiriliyan 2.4 da gwamnatin tarayya ta amince da su.
Wannan na zuwa ne bayan tabbacin da ofishin Akanta Janar ya bayar cewa gwamnati ta amince da biyan kuɗaɗen kwangilar domin aiwatar da manyan ayyuka a fadin ƙasar.
A cewar wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin kakakin majalisar, Chief Levinus Nwabughiogu, ya fitar a Abuja, majalisar ta jaddada bukatar tabbatar da sahihancin ayyukan da aka biya, tare da gargadin gujewa biyan kuɗi ga ayyukan da ba su da amfani ga ‘yan ƙasa.
Mataimakin kakakin Majalisar, Hon. Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin da majalisar ta gudanar da wani zama da gwamnati da ‘yan kwangila a baya, ya ce an cimma matsaya bayan wata zanga-zanga da ‘yan kwangila suka yi.



