Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya shigar da karar wasu manyan jami’ai biyar, kan zargin yin karya a shekaru da nufin tsawaita wa’adin aikinsu.
Daily Trust ta ruwaito cewa Kayode ya shigar da karar ce gaban wata babbar kotu a Abuja, yana zargin jami’an da rage shekaru a takardun su na shaidar haihuwa.
Wadanda babban sufeton ya shigar da karar dai sun hada da mai mukamin AIG, sai CP guda biyu, da kuma DCP baya ga wani ACP, wanda ya ce dukkanin su masu murabus ne.
Sai dai wasu daga cikin wadanda ake kara sun musanta wannan zargi, inda mai shari’a Yusuf Halilu ya sanya ranar 25 ga watan Satumba domin gurfanar da su a kuma fara zaman shari’a.



