Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kudurin Najeriya na karbar bakuncin gasar wasannin Commonwealth na shekarar 2030 a matsayin wani mafarki da ya zama wajibi Najeriya ta cika.
Da yake bayyana hakan a shafinsa na X, shugaban ya ce har zuwa yanzu babu wata kasa a nahiyar Afirka da ta taba karbar bakuncin gasar.
A cewar sa, samun nasara a kudurin, zai isar da sakon cewa Najeriya na da matukar muhimmanci ga ci-gaban kasashe rainon Ingila, kamar yadda Channels TV ya wallafa.



