Wata kotun majistire da ke zaman ta a Ebute Metta a jihar Legas ta bayar da umarnin tsare wasu matasa biyu da ake zargi da satar kayan abinci da kudin su ya kai Naira miliyan 2 da dubu dari 5.
An gurfanar da matasan biyu gaban mai shari’a Folashade Hughes, kan tuhumar haɗa baki da kuma aikata sata, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Mai gabatar da kara daga bangaren ‘yan sanda, ya ce ana zargin su da sace kayan da suka hadar da shinkafa, wake, man girki, kaji, kayan marmari, garin kwaki da dai sauran kayayyaki daga wani kamfani.
Sai dai wadanda ake zargi sun musanta aikata laifukan, inda mai shari’a ta bayar da umarnin tsare su, sai dai akwai damar beli kan Naira dubu dari 5 ga kowannen su.
Ta kuma dage zaman shari’ar har zuwa ranar 14 ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraro.