Jam’iyyar hadaka ta ADC ta bayyana cewa za ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027 ga duk wani ɗan takara daga yankin Arewa ko Kudu, ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.
Wannan matakin ya fito ne bayan taron kwamitin dattawan jam’iyyar na ƙasa da ta gudanar a ranar Alhamis a Abuja, inda kakakin jam’iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa duk masu sha’awar tsayawa takarar sun amince za su mara baya ga duk wanda ya lashe zaben fitar da gwani, domin tabbatar da haɗin kai da nasara a zaben 2027.
Bolaji ya bayyana cewa a halin yanzu ba batun yanki ake tattaunawa ba, sai dai gina ƙarfin jam’iyyar, haka kuma a taron an umurci duk mambobin ADC da ke riƙe da katin wata jam’iyya su yi bayyana ficewarsu daga waccan jam’iyyar.